Kotun Koli Ta Tabbatar Da Hukuncin Daurin Shekaru 12 Da Aka Yiwa Jolly Nyame

10

Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 12 da aka yiwa Jolly Nyame, bisa laifin almundahanar kudade zamanin da yake gwamnan jihar Taraba daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Kotun mai alkalai 5 a wani hukuncin bai daya da ta yanke, karkashin jagorancin mai sharia Mary Odili, tace bata samu dalilin da zai sa ta soke hukunce-hukuncen kotun gurfanarwa da kotun daukaka kara ba, wadanda suka samu Jolly Nyame da laifin almundahanar kudade.

Da take ayyana hukuncin, mai sharia Amina Augie, ta tabbatar da cewa daukaka karar da tsohon gwamnan yayi, yana kalubalantar hukuncin da aka yanke masa, ba ta da tushe bare makama.

Sai dai kotun kolin ta ce kotun daukaka karar tayi kuskure wajen cin tarar Jolly Nyame.

Mai shari’a Amina Augie, daga nan sai ta tabbatar da zaman gidan kason, amma ta wanke Jolly Nyame daga biyan tarar kudi, bisa laifuffukan da ya yiwa jiharsa lokacin da yake gwamna.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × five =