Gwamnatin Tarayya ta Saka Kyautar Kudi Naira Miliyan 36 ga Duk Dan Wanda Ya Samo Maganin Cutar Coronovirus

2

Gwamnatin Tarayya ta kalubalanci masana kimiyya a Najeriya da su samo maganin kwayar cutar Coronavirus wacce a halin yanzu take barazana ga duniya.

Ministan kimiyya da fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu, wanda ya bayar da kalubalen ya kuma yi alkawarin bayar da kyautar kudi Naira Miliyan 36 ga duk wani dan Najeriya masanin kimiyya da ya samo maganin cutar.

Ministan yayi jawabi yayin bikin bankwana da aka shirya domin karrama tsohon daraktan binciken sinadarai a ma’aikatar, wanda ya ajiye aiki a ‘yan kwanakinnan.

Yayi bayanin cewa an shirya bayar da kyautar kudi Naira Miliyan 36 da nufin karfafa gwiwa ga masana kimiyya na cikin kasa su dukufa wajen bincike, inda ya tabbatar musu cewa gwamnatin tarayya tana goyon bayan ayyukan bincike da cigaba.

Ministan daga nan sai ya bukaci masana kimiyya da su tashi tsaye wajen lalubo mafita daga matsalolin dake addabar bil’adama domin nunawa duniya cewa Najeriya tana da karfin magance matsalolin bil’adama, ba wai a cikin kasa kadai ba, har ma a fadin duniya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − 2 =