Mahara a Ranar Laraba da Dare Sun Bude Wuta Kan ‘Yan Kasuwa a Jihar Kaduna

8

Wasu wadanda ake zargin mahara ne a jiya Laraba da dare sun bude wuta kan ‘yan kasuwa a kasuwar Maro dake masarautar Adara a yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda suke kashe mutane 7.

Lamarin ya auku da misalin karfe 7.30 na dare yayin da ‘yan kasuwar ke kokarin rufe shagunansu.

Wata majiya dake kusa da Hakimin Kufana ta tabbatar da aukuwar lamarin yau Alhamis, inda tace maharan sun bude wuta kan ‘yan kasuwar, inda suke kashe mutane 7 tare da jikkata wasu da ba a san adadinsu ba.

Majiyar tace maharan sun kai farmaki zuwa kasuwar a wata mota inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Da ake nemi jin ta bakin kakakin rundunar ‘yansanda na jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya bayar da tabbacin cewa zai nemi bayanin harin kafin ya mayar da martani.

Harin ya auku kwana 1 bayan wasu mahara sun kai farmaki zuwa kauyen Bakali a gundumar Fatika dake karamar hukumar Giwa a jihar ta Kaduna, inda suka kashe mutane 21, cikinsu har da mutane 16 ‘yan gida daya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen − six =