Amnesty International ta Zargi Sojin Najeriya da Kone Wasu Kauyuka a Jihar Borno

13

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta Zargi Sojojin Najeriya da Kone Wasu Kauyuka a Jihar Borno, daya daga cikin jihoshin da rikicin Boko Haram ya yiwa mummunan illah a yankin Arewa maso Gabas.

A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, kungiyar ta kuma yi zargin cewa jami’an tsaro sun raba mutane da muhallansu, a kauyukan da lamarin ya shafa, a mayar da martani dangane da karuwar hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram na baya-bayannan.

Duk da hukumomin soji sun karyata zarge-zargen, kungiyar kare hakkin bil’adaman tace ta samu bayananta ne daga tattaunawar da tayi da mazauna kauyen da abin ya shafa da kuma binciken hotunan tauraron dan’adam.

Kungiyar tayi nuni da cewa yan Boko Haram din sun karfafa ayyukansu a yankin tun daga watan Disambar 2019, musamman akan babban titin da ya hada Birnin Maiduguri na jihar Borno, da Damaturu na jihar Yobe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen + 2 =