Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Sabbin Kayan Sarki Ga Hukumar Gyaran Da’a Ta Najeriya

10

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Sabbin Kayan Sarki Ga Hukumar Gyaran Da’a Ta Najeriya.

Shugaban hukumar, Ja’afaru Ahmed, shine ya sanar da wannan cigaban yayin bikin kaddamar da ginin gudanarwa na makarantar ma’aikatan hukumar da ke Abuja.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Augustan bara ya sanya hannu akan sabuwar dokar gyaran da’a ta shekarar 2019, wacce ta shafe dokar gidajen yari ta 2018, tare da sauya sunan hukumar gidajen yarin Najeriya zuwa hukumar gyaran da’a ta Najeriya.

Ja’afaru Ahmed yace daukar wannan matakin wani bangare ne na sabuwar dokar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu.

Ja’afaru Ahmed yace akwai sabbin kirkire-kirkire a sabuwar dokar kamar su ilimin ma’aikata da kiwon lafiya da gidaje, inda ya kara da cewa kula da walwalar jami’a da dakarun hukumar na da muhimmanci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × 3 =