Fadar Shugaban Kasa Ta Musanta Labarin Da Ke Cewa Shugaban Kasa Buhari Zai Yi Tafiya Zuwa Kasar Ingila

4

Fadar Shugaban Kasa ta sanar da cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da iyalansa da ministoci da shugabannin tsaro, suna shan suka daga wadanda aka kira da dillalan yada labaran karya.

A wata sanarwar da kakakin shugaban kasa, Mista Femi Adesina ya fitar, ya bayar da misali da wani labari dake ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi tafiya ta kwanaki ashirin zuwa Ingila, a matsayin daya daga cikin labaran kanzon kurege.

Da yake jawo hankalin jama’a akan sabbin abubuwan dake faruwa tare da gargadinsu akan suke taka-tsan-tsan wajen amincewa da labaran da ba a tantance su ba, musamman a kafafen sada zumunta na zamani, Femi Adesina, yace wannan ce hanya kadai da za ayi maganin wannan sabon kalubalen na suka ga shugaban kasar da iyalan sa da ministoci da kuma jami’an tsaron kasar nan..

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi taka-tsantsan da labaran da suka amince da su tare da hana kawunansu yada rahotannin da basu tabbatar da sahihancinsu ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 5 =