Shugaba Buhari ya Kaddamar da Ayyukan da Gwamna Akerodolu na Jihar Ondo ya Aiwatar

5

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da ayyuka guda biyu wadanda gwamnatin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ta aiwatar.

Shugaban kasar wanda yaje garin Ore, ya kaddamar da manyan ayyukan guda biyu, rukunin masana’antu na Ore da kuma gadar sama ta Ore.

Ziyarar ta shugaban kasa wani bangare ne na bukukuwan cikar gwamnatin jihar shekaru 3.

Gwamna Rotimi ya bukaci dukkan mutanen jihar da su yi amfani da lokacin bikin wajen shiga bukukuwan da aka shirya.

Tuni gwamnatin jihar ta ayyana cewa yau ranar hutu ce.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × four =