Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Bukatar Sake Bibiyar Hukuncinta

10

Kotun Koli tayi watsi da bukatun sake bibiyar hukuncinta na ranar 13 ga watan Fabrairu, wanda ya soke nasarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Bayelsa da ya gabata.

Zaman kotun mai alkalai 7, karkashin jagorancin mai shari’ah Sylvester Ngwuta, ya bayyana bukatar da jam’iyyar APC ta shigar tare da dan takararta a zaben, David Lyon, a matsayin abu mai wuyar sha’ani da ban tsoro wanda kuma yaci zarafin tsarin aikin kotuna.

Mai shari’ah Amina Augie wacce ta karanta hukuncin, tace bukatar wacce ke neman kotun kolin ta sake zaman akan hukuncin da ta riga ta yanke wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.

Ta dage kan cewa idan aka amince da bukatatun, hakan ya karya dokar cewa kotun ce karshen shari’ah.

Tace amicewa da bukatun zai bude kofar neman sake bibiyar hukunce-hukuncen da kotun kolin ta zartar.

Kotun kolin ta bayar da tarar kudi Naira Miliyan 10 wanda lauyoyin APC da na dan takararta, David Lyon, zasu biya da kansu. Kotun ta zartar da hukuncin cewa dukkan lauyoyin biyu zasu biya kudi Naira Miliyan 10 ga dukkan bangarori ukun da suke kara, jam’iyyar PDP da Gwamnan Jihar Bayelsa da kuma mataimakinsa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × one =