Aminu Ado Bayero Ne Sabon Sarkin Kano

12

An sanar da Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin sabon sarkin Kano. Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, shine ya sanar da hakan a yau, awanni kadan bayan sauke Muhammadu Sanusi na 2 daga kan karagar mulki.

Usman Alhaji yace nadin yana bisa tanadin dokar masarautu ta jihar Kano ta shekarar 2019.

Sakataren gwamnatin yace masu nada sarki a masarautar Kano su 4, tunda farko sun bayar da shawarar nadin Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin Kano.

Aminu Ado Bayero yanzu shine sarki na 15 a zuri’ar Fulani a Kano.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 − 13 =