Ganduje Ya Tsige Sarkin Kano Sanusi II

29

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta sanar da tsige Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na 2.

Darakta-Janar na yada labaran gwamnatin Kano, Salihu Yakasai, shine ya sanar da tsigewar a shafinsa na Tuwita.

Sarki Sanusi ya hau karagar mulki a shekarar 2014, biyo bayan rasuwar Alhaji Ado Bayero. Kakansa, Muhammadu Sanusi na 1 yayi mulkin Kano daga 1953 zuwa 1963, yayin da Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello ya tsige shi. Mahaifinsa, Aminu Sanusi, shine Ciroman Kano a da.

Kafin hawansa mulki, Sanusi masanin tattalin arzikine kuma ma’aikacin banki. Ya rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kasa, CBN, daga 2009 zuwa 2014, lokacin da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dakatar da shi bayan ya fallasa bacewar kudi dala biliyan 20 daga lalitar gwamnatin tarayya.

Sarkin ya sha sa’insa da gwamna tun bara, bisa zargin cewa ya mara baya ga dan takarar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

Tun daga wancan lokacin ake ta binciken sarkin kan zargin rashawa, yayin da aka raba masarautarsa zuwa gida 5 domin rage masa karfin iko.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 − one =