Gwamnatin Tarayya Na Kokarin Samun Dala Biliyan 100 Daga Kayayyakin Da Ba Mai Ba

10

Gwamnatin Tarayya karkashin shirinta na bunkasa kudaden shiga ta hanyoyin da ba na mai ba, ta tsara wani shirin mai dogon zango na samun kudi kimanin dala biliyan 100 daga manyan kayayyakin da ba na mai ba, cikin shekaru 10 masu zuwa.

Babban daraktan hukumar habaka fitar da kayayyaki kasashen ketare, Mista Segun Awolowo, wanda ya zanta da manema labarai, yace shirin na bunkasa kudaden shiga ta hanyoyin da ba na mai ba zai kara akalla dala biliyan 150 ga asusun ajiye kudaden waje na Najeriya cikin shekaru 10 masu zuwa.

Kayayyakin sun hada da auduga da shinkafa da fata da zinare da waken suya da sukari da koko da sinadarai da takin zamani da man ja da roba da simini da tumatur da ayaba da lemo da kashu da rogo da ridi da barkono da citta da sauransu.

Awolowo yace ana sa ran shirin zai samar da ayyukan yi akalla dubu 500 kowace shekara, sanadiyyar karuwar ayyukan sarraffawa tare fitar da kayayyaki kasashen ketare, lamarin da zai taimaka wajen cimma muradan karni.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

16 + 7 =