Majalisar Dattawa ta Gabatar da Kudirin Da Zai Cire Rigar Karaya Daga Mataimakin Shugaban Kasa, Gwamnoni da Mataimakansu

4

Majalisar dattawa ta kirkiri wani kudiri wanda zai cire rigar kariya daga mataimakin shugaban kasa da gwamnonin jihoshi tare da mataimakansu, muddin suka yi wadaka da dukiyar al’umma.

Shugaban kasa da mataimakinsa da gwamnonin jihoshi tare da mataimakansu a halin yanzu suna samun kariya daga tuhuma yayin da suke kan karagar mulki.

Sai dai, kudirin na majalisar dattawa na shirin sauya hakan, amma ya ware shugaban kasa daga cikin wadanda abin zai shafa.

Ana nufin kudirin zai sauya dukkan sassan kundin tsarin mulki, yadda zai bayar da dama ga hukumomin tsaro su kama tare da hukunta mataimakin shugaban kasa da gwamnoni da mataimakansu, muddin suka yi sama da fadi da dukiyar jama’a.

Shugaban kwamitin majalisar kan bibiyar kundin tsarin mulki na 1999, wanda kuma shine mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Obi Omo-Agege, shine ya gabatar da kudirin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

six + 16 =