Shugaba Buhari Ya Tabbatar Da Jajircewar Najeriya Wajen Dakile Yaduwar Cutar Coronavirus

6

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da jajircewar Najeriya wajen kokarin da duniya ke yi na dakile yaduwar cutar coronavirus.

Yayi alkawarin ne a sakonsa na jaje ga shugabannin kasashe kawayen Najeriya na huldar diplomasiyya guda 3, wadanda a baya-bayannan suka gamu da iftila’in cutar.

Shugaban kasar ya aika da sako ga shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani da na Koriya ta Kudu, Mun Ja’in, tare da fira-ministan Italiya, Juseffo Konte, inda yake bayyana jajantawar da gwamnatin tarayya ke yi musu.

A sakonnin, wanda aka yi bayaninsu cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya fitar, tace gwamnatin Najeriya za ta cigaba da taka rawarta ga al’ummarta, wajen tabbatar da cewa an dakile yaduwar cutar ta coronavirus.

Shugaban kasar ya kuma karfafawa ‘yan Najeriya gwiwa, inda ya bukaci da su tallafawa mutanen kowace kasa wadanda suke zaune a Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 + 3 =