Fadar Shugaban Kasa Ta Musanta Cewa Buhari Yana Da Hannu A Sauke Sanusi

71

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana kokarin danganta sauke tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 2 ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin cin zarafi da siyasa.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wata fira da sashin Hausa na BBC, yayi zargin cewa shugaban kasa Buhari ne ya bayar da umarnin sauken tsohon sarkin.

Amma a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya fitar, fadar shugaban kasar tace Shugaba Buhari bashi da hannu a rikicin na Kano, inda ya nanata cewa ba a san shi da tsoma baki a harkokin jihoshi ba.

Fadar shugaban kasa ta kuma zargi ‘yan siyasa daga bangaren adawa da yada abinda ta kira jita-jitar siyasa, cewa ba adalchi bane masu yin hakan suke yada jita-jitar akan shugaban kasa.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa matsalolin dake zagaye da nadi da iko akan sarakunan gargajiya an damka su ga mahukuntan gwamnatocin jihoshi a kundin tsarin mulkin kas ana 1999.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × three =