Filin Jiragen Saman Dakon Kaya Na Kasa Da Kasa Na Yobe Zai Fara Aiki Wata Mai Zuwa

5

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, yace filin jiragen saman dakon kaya na kasa da kasa na Yobe, zai fara aiki wata mai zuwa.

Gwamnan yace ya samu tabbaci daga ‘yan kwangilar dake aikin, cewa za a mikawa gwamnatin jihar aikin a karshen watan gobe na Afrilu.

Yace gwamnatin daga nan zata kaddamar da shi a watan Mayu.

Mai Mala Buni ya sanar da hakan bayan ziyarar gani da ido zuwa filin jiragen saman wanda ake aikin ginawa.

Tunda farko, kwamishinan sufuri da makamashi, Abdullahi Kukuwa, da yake zagayawa da gwamnan cikin filin jiragen saman, yace aikin farfajiyar saukar jiragen ya kai kashi 70 cikin 100, yayin da aka kusa kammala aikin sauran gine-ginen filin jiragen saman.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 + sixteen =