An Gano Babu Cutar Coronavirus A Jikin Mutum Na Biyu Da Ake Zargin Ya Kamu Da Cutar A Najeriya

8

Ministan lafiya, Osaji Ehanire, yace an gwada mutum na biyu da ake zargin ya kamu da cutar coronavirus a Najeriya, kuma an gano babu cutar a jikinsa.

Ehanire yace kawo yanzu kasarnan ta samu rahoton bullar cutar a jikin mutane biyu ne kacal, na farko wanda ya kawo cutar kasarnan, dan Italiya wanda ya shigo kasarnan, sai mutum na biyu wanda yayi mu’amala da dan Italiyan wanda ya kawo cutar.

A wani labarin kuma, ministan yace kasarnan zata cigaba da saka ido akan cutar, musamman a jikin wadanda suke shigowa kasarnan ta filin jiragen sama.

Yace hadarin shigowa da cutar kasarnan yafi yawa tsakankanin masu shigowa ta jiragen sama, akan masu zuwa ta jiragen ruwa ko a motoci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 − 8 =