Hukumar Immigration Na Daukar Ma’aikata

140

Hukumar Shige ta Fice ta Kasa, Immigration, tace tana neman daukar wadanda suka cancanta aiki a hukumar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sunday James, shine ya sanar da daukar aikin a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Wannan yazo ne bayan hukumar dake kula da civil defence da gidajen gyaran da’a da ‘yan kwana-kwana da shige da fice, ta amince da daukar aikin.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, shine ya amince da daukar aikin.

Kamar yadda yake a wani hoto da hukumar ta wallafa, guraben matsayin da ake neman ma’aikatan sune na Sufeto da Sufritanda da kuma Assistant.

A cewar hukumar, ana tsammanin wadanda zasu nemi aiki ya zamto suna da ilimin sarrafa na’ura mai kwakwalwa, kasancewar hanyoyin daukar aikin zai hada da rubuta jarabawa a komfuta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 + 12 =