Hukumar Immigration Ta Sauya Shafinta Na Yanar Gizo Na Daukar Ma’aikata

47

Hukumar Shige da Fice ta Kasa Immigration ta sanar da canja shafinta na yanar gizo domin daukar ma’aikata.

Kakakin hukumar, Sunday James, shine ya sanar da haka yau da safe.

Yace hukumar ta canja shafin zuwa www.immigrationrecruitment.org.ng wanda a halin yanzu yake aiki, inda ya kara da cewa an dauki matakin ne domin gyara shafin yadda masu neman aikin zasu iya shiga sosai.

Sunday James ya tunatarwa da jama’a cewa aikin daukan ma’aikatan kyauta ne, kuma in banda canjin shafin, dukkan bayanan da aka dora a sanarwar daukan aikin, suna nan basu sauya ba.

Sai dai hukumar bata ce uffan ba dangane da kara wa’adin ranar rufe cike shafin neman aikin, sanadiyyar matsalar da tsohon shafin ya bayar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × 5 =