COVID-19: Aisha Buhari Ta Yi Kiran Da A Tsayar Da Ayyukan Komai da Komai a Kasarnan

16

Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, tayi kiran da a tsayar da ayyukan komai da komai a kasarnan, bayan wadanda suka kamu da cutar coronavirus sun kai 36, tare da wani mutum guda da ya mutu sanadiyyar cutar a kasarnan, a yau Litinin.

Aisha Buhari ta bayar da misali da gwamnonin jihoshin da suke rufe makarantu, amma suna barin iyayen yaran suna cigaba da zuwa aiki.

Tayi nuni da cewa duk da matakin da gwamnonin suka dauka abin a yaba ne, zai zama aikin baban giwa muddin aka bar iyayensu suka cigaba da zuwa aiki.

An rawaito cewa daya daga cikin ‘ya’yan shugaban kasa, wacce a yan kwanakin nan ta dawo daga Ingila, an killaceta, bisa shawarar cibiyar kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya.

Aisha Buhari ce ta sanar da killace ‘yar ta ta a makon da ya gabata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 2 =