Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU Ta Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

8

Kungiyar Malaman Jami’o’in kasarnan, a yau Litinin, ta ayyana tafiya yajin aikin sai baba ta gani, bisa biyan albashi karkashin tsarin IPPIS, tare da kin aiwatar da yarjejeniyar 2009.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ya sanar da tafiya yajin aikin yayin taron manema labarai a helkwatar kungiyar dake Abuja.

Yayi nuni da cewa gwamnati taki magance matsalolin a kungiyar ta zayyana.

Kungiyar, a ranar 9 ga watan Maris, ta ayyana tafiya yajin aikin gargadi na makonni 2.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nineteen − 14 =