Abba Kyari Ya Kamu Da Coronavirus Amma Babu Cutar a Jikin Shugaba Buhari

19

Ba a samu cutar coronavirus a jikin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba, biyo bayin gwajin cutar da cibiyar kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya tayi masa.

Cibiyar ta sanar da shugaban kasar sakamakon gwajinsa cewa bashi da cutar, yau da safe a Abuja.

A cewar wasu majiyoyi a fadar shugaban kasar, an yiwa shugaban kasar gwajin bayan gwajin da aka yiwa shugaban ma’aikatansa, Abba Kyari, ya nuna cewa yana dauke da cutar a jiya Litinin.

Abba Kyari yayi tafiya zuwa Jamus ranar Asabar, 7 ga watan Maris, inda ya dawo bayan sati guda, ranar Asabar, 14 ga watan Maris, amma bai nuna alamun cutar ba. Ance ya halarci zaman tattaunawa kan dakile cutar ta covid-19 a Najeriya, wanda aka yi ranar Lahadi, inda aka bayar da rahoton cewa ya fara tari.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

six + three =