Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo Baya Dauke Da Cutar Coronavirus

3

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbaji baya dauke da cutar coronavirus, a cewar mai bawa shugaban kasa shawara kan al’amuran siyasa, Sanata Babafemi Ojudu.

Ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa gwajin da aka yiwa Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa babu cutar a jikinsa.

Sai dai bai fadi lokacin da aka gudanar da gwajin ba.

Kazalika, kakakin Yemi Osinbajo, Mista Laolu Akande, ya tabbatar da labarin.

Yemi Osinbajo ya kange kansa da kansa ranar Litinin da dare, biyo bayan rahotannin dake cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Mallam Abba Kyari, ya kamu da cutar ta coronavirus.

Mataimakin shugaban kasar na daya daga cikin jami’an gwamnati wadanda Abba Kyari yayi mu’amala dasu kai tsaye, bayan dawowarsa daga kasashen Jamus da Masar a makon da ya gabata.

Mataimakin shugaban kasa bai je aiki fadar shugaban kasa ba, jiya Talata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve − eight =