An Sayar Da Kowace Dala Daya Akan Naira 402 Jiya Juma’a

8

An sayar da kowace Dalar Amurka guda akan Naira 402 jiya Juma’a a sashen ‘yan canjin kudade na kasuwar musayar kudaden waje.

Wannan ya biyo bayan dakatar da sayar da kudaden waje ga ‘yan canjin kudade da babban bankin kasa CBN yayi.

Kungiyar ‘yan canjin kudade a Najeriya ta bukaci babban bankin kasa CBN da ya bata hutun kasuwanci biyo bayan kalubalen da ake cigaba da fuskanta a tattalin arzikin kasa da na duniya baki daya, sanadiyyar illar cutar coronavirus.

Bankin na CBN ya amince da bukatar ta kungiyar ‘yan canjin kudaden inda ya basu hutun kasuwanci na makonni 2.

A cewar ‘yan canjin, an samu raguwar bukatar kudaden waje sosai saboda illar annobar covid-19 ga tattalin arziki, kasancewar an rufe kamfanoni da shagunan kasuwanci dayawa, kuma mutane dayawa sun dena tafiye-tafiye.

Kazalika Naira ta fuskanci koma baya sanadiyyar farashin danyen mai wanda ya fadi kasa wanwar a kasuwannin duniya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 + four =