Coronavirus: Gwamnatin Katsina Ta Rufe Dukkan Hanyoyin Shiga Jihar

10

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya rufe dukkan hanyoyin shiga jihar, wadanda suka hada da jamhuriyar Nijar, a matsayin wani matakin magance yiwuwar yaduwar coronavirus a jihar.

Jihar ta Katsina tayi iyaka da Jigawa da Kano da Kaduna da Zamfara da kuma jamhuriyar Nijar daga Arewa.

Kwamishinan labarai, al’adu da harkokin cikin gida, Abdulkarim Sirika, shine ya sanar da umarnin jiya Juma’a.

Abdulkarim Sirika, wanda shine shugaban kwamitin karta kwana wajen kula da yaduwar cutar covid-19 a jihar, yace matakin ya fara aiki daga karfe 6 na safiyar yau Asabar.

Abdulkarim Sirika yace tankokin mai da motocin dake dakon kayan abinci da sauran kayayyakin da ake bukata sosai, za a barsu shiga jihar bayan anyi musu bincike akan iyakoki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − 5 =