Kawo Yanzu Mutane 81 Ne Suka Kamu Da Cutar Covid-19 A Najeriya Bayan An Sanar Da Kamuwar Wasu Sabbin Mutane 11

6

Kawo yanzu mutane 81 ne suka kamu da cutar covid-19 a Najeriya, bayan cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasa ta sanar da kamuwar wasu sabbin mutane 11 jiya Juma’a.

Jihar Enugu a Kudu Maso Gabashin kasarnan ita ma ta shiga sahun jihoshin kasarnan, da aka tabbatar da bullar annobar.

An sanar da sabbin wadanda suka kamun su 11, kasa da awanni 4 bayan hukumomin lafiya sun sanar da sabbin mutane 5 da suka kamu da cutar.

Wannan ya kawo yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar zuwa 16 a jiya Juma’a kadai. Wanda kuma shine adadi mafi yawa na wadanda suka kamu cikin rana guda, tun bayan da kasar ta sanar da mutum na farko da ya fara kawo cutar a watan Fabrairu.

Mutumin na farko, dan kasar Italiyan nan, wanda ya ziyarci wani kamfanin siminti a jihar Ogun, tuni ya samu sauki kuma aka sallame shi daga asibiti. Karin wasu mutane biyu da suka kamu da cutar, anyi musu magani tare da sallamarsu, yayin da aka samu mutum guda wanda cutar ta hallaka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 − three =