Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki Sun Amince Da Bayar Da Wuta Kyauta Tsawon Watanni Biyu

11

Kamfanonin rarraba wutar lantarki sun sanar da cewa suna goyon bayan yunkurin majalisun kasa da bangaren zartarwa na tarayya cewa a bawa ‘yan Najeriya wutar lantarki a kyauta ta watanni 2.

Da suke magana karkashin kungiyarsu, kungiyar masu rarraba wutar lantarki na Najeriya, kamfanonin rarraba wutar lantarkin sun bayyana cewa ya kamata a samar da tsare-tsaren bayar da wuta kyauta, kuma a bayyanawa jama’a a lokacin da ya dace.

Zababben Daraktan kungiyar, Sunday Oduntan, shine ya bayyana haka cikin wata sanarwar da aka fitar a Abuja.

Ya nanata jajircewar kamfanonin rarraba wutar lantarki wajen inganta ayyukansu a kasarnan, lokacin annobar coronavirus da bayanta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × 5 =