Karin Mutane 22 Sun Kamu Da COVID-19 a Najeriya

6

An sanar da karin mutane 22 da suka kamu da COVID-19 a Najeriya, cutar da ta kashe mutane 6 a kasarnan kawo yanzu.

Cibiyar kula da yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da cewa jumillar mutanen da cutar ta kama a kasarnan sun karu daga 254 shekaranjiya Talata da dare zuwa 276 jiya Laraba da dare.

An samu sabbin mutane 15 da suka kamu a Lagos, 4 a babban birnin tarayya, 2 a Bauchi, yayin da aka samu mutum guda a Edo.

Kawo yanzu mutanen cutar ta kwantar su 44 aka sallama daga asibiti bayan sun samu sauki, yayin da cutar ta hallaka mutane 6.

Kididdigar alkaluman wadanda cutar ta kama a kasarnan ya nuna cewa a jihar Lagos an samu mutane 145, babban birnin tarayya 54, Osun 20, Oyo 11, Edo 12, Bauchi 8, Akwa Ibom 5, Kaduna 5, Ogun 4, Enugu 2, Ekiti 2, Ribas 2, Kwara 2, Benue 1, Ondo 1, Delta 1 da kuma mutum 1 a Katsina.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five + eighteen =