Mutane 938 Coronavirus Ta Kashe Cikin Awanni 24 A Birtaniya

9

Yawan mutanen da cutar COVID-19 suka hallaka a Birtaniya ya karu da mutane 938 cikin awanni 24.

Hakan yasa alkaluman na baya-bayannan suka zama mafiya yawa yawa cikin kwana guda, tun bayan barkewar cutar a kasar.

A cewar hukumar lafiyar kasar, kimanin mutane dubu 60 da 733 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, yayinda ta kashe mutaen dubu 7 da 97.

Kawo shekaranjiya Talata, yawan mutanen da cutar ta hallaka dubu 6 da 159 ne, bayan ta harbi mutane dubu 55 da 242.

Alkaluman na gwamnati, na mutanen da suka mutu a asibiti ne, kuma bai hada da wadanda suka mutu a cikin unguwanni da gidajensu ba, wanda hakan ya nuna cewa yawan wadanda cutar ta kashe zasu iya fin haka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − 19 =