Cigaba Da Barkewar Zazzabin Lassa a Najeriya, Kawo Yanzu Ya Kashe Mutane 188 A 2020

11

A cigaba da barkewar zazzabin Lassa a Najeria, kawo yanzu cutar ta kashe mutane 188 tun farkon shekararnan, a cewar cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC.

Najeriya a yanzu tana yaki da cututtuka biyu masu saurin kisa, wato zazzabin Lassa da Coronavirus.

Yayin da Coronavirus ta kasance sabuwar cutar dake addabar duniya baki daya, zazzabin Lassa ya zamo annoba a Najeriya, inda kasar ke yaki da shi kowace shekara tsawon shekaru 50 da suka gabata.

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, tace tun farkon barkewar zazzabin Lassa, an samu mutane 963 da suka kamu da zazzabin, wanda ya hallaka mutane 188.

A makon da ya gabata, jumillar yawan wadanda zazzabin ya kashe sun kai 185, abin nufi, mutane 3 ne suka mutu saboda zazzabin cikin satin da ya gabata.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + eighteen =