Shugaba Deby Na Chadi Ya Yiwa Najeriya Shagube Bisa Sakin Mayakan Boko Haram

13

Shugaban Kasar Chadi, Idriss Deby, ya umarci sojojinsa da kada su kyale takwarorinsu na Najeriya su saki mayakan Boko Haram da aka kama.

Sojojin na Chadi a makon da ya gabata sun kaddamar da hare-hare akan mayakan na Boko Haram a yankin dajin Sambisa na Chadi, wanda ke karkashin ikon Boko Haram.

An kashe mayakan na Boko Haram da dama, kuma sojojin Chadi sun kwace iko da wajen da ‘yan Boko Haram ke ajiye makamansu a yankin.

A wani faifan bidiyo da ake ta yadawa, an ga Shugaban Kasar yana gayawa sojojinsa cewa muddin aka saki mayakan na Boko Haram, zasu dawo Chadi domin cutar da su.

A watan Maris na 2015, Idris Deby yace babu Najeriya a yakin da ake yi da Boko Haram.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine − 4 =