NCDC Ta Tabbatar Da Samun Sabbin Mutane 87 Da Suka Kamu Da Corona a Najeriya

4

An tabbatar da sabbin mutane 87 da suka kamu da cutar corona a Najeriya, a cewar rahoton cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC.

Sabbin mutanen da suka kamu suna jihoshi 9 dake fadin kasarnan. Hakan ya kawo yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasarnan zuwa 1,182.

Kididdigar sabbin wadanda suka kamun ya nuna cewa an samu mutane 33 a Lagos, 18 a Borno, 12 a Osun, 9 a Katsina, 4 a Kano, 4 a Ekiti, 3 a Edo, 3 a Bauchi da kuma 1 a Imo.

Har yanzu Lagos ce inda barkewar cutar tafi kamari a Najeriya, yayin da aka samu mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar Imo, tun bayan barkewarta a kasarnan.

Cibiyar ta NCDC tace zuwa karfe 11 da minti 55 na dare a ranar Asabar, akwai mutane 1,182 da aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya. Daga cikin adadin, mutane 222 sun warke daga cutar kuma an sallamesu daga asibiti, yayin da yawan wadanda cutar ta hallaka suka karu zuwa 35 daga 32 da aka bayar da rahoton cutar ta kashe a ranar Juma’a.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen + seven =