An Samu Mafiya Yawan Mutanen Da Suka Kamu Da Corona A Rana Guda a Najeriya

5

A ranar da gwamnatin tarayya ta sassauta dokar kulle a manyan biranen kasarnan, an samu mafiya yawan mutanen da suka kamu da cutar corona a rana guda, inda yawan wadanda suka kamu a jiya ya kai 245.

Hukumar dakile bazuwar cututtuka ta kasa NCDC ita ta sanar da haka a jiya da dare. Alkaluman sun kawo jumillar wadanda suka kamu da cutar a kasarnan zuwa dubu 2 da dari 8 da 2, a cewar hukumar.

Kididdigar sabbin alkaluman sun nuna cewa Lagos ce kan gaba da mutane 79, inda Katsina ta biyo baya da mutane 37 sai Jigawa da 32 da Kano da 23 sai kuma babban birnin tarayya da mutane 19.

A jiya litinin din, an samu rahoton wadanda suka kamu da cutar a jihoshi 16 na kasarnan.

Mutane 245 da suka kamu a jiyan sun kawo jumillar wadanda suka kamu da cutar a kasarnan zuwa dubu 2 da dari 8 da 2, cikinsu har da mutane 417 da suka warke aka sallama, da kuma 92 da cutar ta hallaka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve + 5 =