Shugaba Buhari Ya Bukaci Hadin Kan Kasashen Duniya Kan Cutar Corona

7

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace hadin kan kasa da kasa ne kadai zai kawo karshen illolin annobar corona, inda yake tabbatar da cewa gwamnatin tarayya zata kara azama wajen sa’ido da gwaji tare da killace karin mutane, musamman a cikin al’umma.

Shugaba Buhari wanda ya halarci taron ganawa ta bidiyon kai tsaye na shugabannin kasashe, yace akwai bukatar amfani da dabaru a matakan kasashe da yankuna da ma duniya wajen magance annobar, wacce a cewarsa, ta daidaita bil’adama tare da haifar da tabarbarewar zamantakewa da rayuwar yau da kullum da ma tattalin arzikin duniya.

Shugaba kasar yace har yanzu akwai danyen aiki a gaban duniya, kuma akwai bukatar a kara azama wajen rage illar cutar corona.

Shugaban kasar ya shaidawa shugabannin kasashen cewa dole a jinjinawa rawar da majalisar dinkin duniya tare da hukumar lafiya ta duniya WHO ke takawa wajen yaki da annobar, domin amfanuwar dukkan kasashe mambobin majalisar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − 8 =