Gwamnatin Tarayya Ta Dage Kan Ciyar Da Dalibai ‘Yan Makaranta a Gida

6

Ministar Agaji da Kula da Annoba, Sadiya Umar Farouq, ta sanar da cewa Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihoshi sun shirya tsaf wajen fara shirin ciyar da yara ‘yan makaranta a gidajensu.

Da take jawabi a a taron manema labarai na kwamitin karta kwana na shugaban kasa akan cutar corona, Sadiya Farouq tace gwamnati tayi garanbawul a shirin ciyar da ‘yan makaranta ta yadda za’a tabbatar da cewa an ciyar da yara ‘yan makaranta a gidajensu duk da dokar kulle.

Ta yi nuni da cewa ma’aikatarta, tare da hadin gwiwa da gwamnatin jihoshi sun samar da tsarin aiwatar da ciyarwar a gida, inda ta kara da cewa za a fara ciyarwar nan bada dadewa ba.

Ministar ta yi bayanin cewa za a kai abincin gida-gida, kasancewar za a bayar da katin shaidar karbar abincin a lokuta daban-daban saboda a kauracewa cunkoso.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × four =