Kamfanin NNPC Ya Rage Farashin Mai A Guraren Dauko Man

10

Kamfanin Mai na Kasa NNPC ya sanar da ragin farashin man fetur kudin sari daga Naira 113 da kobo 28 kowace Lita zuwa Naira 108 kowace Lita.

Farashin kudin sari shine farashin da ake bawa ‘yan kasuwa su sayar, a guraren ajiyar mai.

Kamfanin yace ragin farashin ya shafi dukkan albarkatun da yake samarwa da kuma ayyukansa.

Manajan Daraktan Kamfanin wanda yake kula da huldar jama’a, Kenni Obateru, ya jiyo Manajan Darakta na Kamfanin Albarkatun Man Fetur, Musa Lawan, na cewa sabon farashin da aka bawa ‘yan kasuwar, ‘yar manuniya ce ta dabarun kasuwancin kamfanin.

Sai dai, kamfanin bai bayyana cewa ko rage farashin da aka bawa ‘yan kasuwar, zai jawo raguwar farashin mai a gidajen mai ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 4 =