Yawan Mutanen Da Suka Kamu Da Corona A Najeriya Sun Haura 3,000 Bayan Kwanaki 100

6

Yawan mutanen da suka kamu da cutar corona a Najeriya sun haura dubu 3 bayan cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da samun sabbin mutane 195 da suka kamu da cutar.

Wannan ya kawo jumillar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasarnan zuwa 3,145.

Hukumar a jiya da dare tace an samu sabbin mutane 195 da suka harbu a jihoshi 13. Kuma dama an taba samu wadanda suka kamu a baya a dukkan jihoshin.

Jiya Laraba aka cika kwanaki 100 tun bayan da aka samu mutum na farko da ya kamu da cutar corona a Najeriya.

Sabbin mutane 195 da aka bayar da rahoton sun kamu a jihoshi 13 wadanda suka hada da 82 a Lagos da 30 a Kano da 19 a Zamfara da 18 a Sokoto da 10 a Borno da 9 a Babban Birnin Tarayya da 8 a Oyo da 5 a Gombe da 4 a Ogun da 3 a Katsina da 1 a Kaduna da kuma 1 a Adamawa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two + sixteen =