An Samu Sabbin Mutane 381 Da Suka Kamu Da Cutar Corona Ranar Alhamis A Najeriya

5

Jiya Alhamis an samu mutanen da suka kamu da cutar corona a Najeriya da adadi mafi yawa a rana guda, tun bayan samun wanda ya fara kawo cutar, inda cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da sabbin mutane 381 wadanda cutar ta harba.

Da sabbin alkaluman, yawan wadanda suka kamu da cutar a kasarnan sun karu zuwa 3,526 daga 3,145 da aka bayar da rahoton sun kamu kawo shekaranjiya Laraba.

Sabbin mutanen 381 da suka kamu an same su a jihoshi 18, inda aka samu mutane 183 a Lagos, 55 a Kano, 44 a Jigawa, 19 a Zamfara, 19 a Bauchi, 11 a Katsina, 4 a Sokoto, 3 a Oyo, 3 a Rivers, 2 a Naija, 1 a Akwa Ibom, 1 a Enugu da kuma 1 a Filato.

An samu karin yawan wadanda cutar ta harba a jiya, idan aka kwatanta da mutane 195 da aka bayar da rahoton sun harbu a shekaranjiya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve − 7 =