‘Yan Najeriya 300 Za A Kwaso Daga Birtaniya Ranar Juma’a

9

Kimanin ‘yan Najeriya 300 da suka makale a Birtaniya za a kwaso zuwa gida a wani jirgin saman da aka yi shatarsa, a yau Juma’a.

Wadanda za a kwaso da zarar sun sauka a Abuja za a killacesu tsawon kwanaki 14 tare da yi musu gwajin cutar corona. Suna daga cikin ‘yan Najeriya 4,000 da ake aikin kwasowa daga kasashen waje.

Rukunin farko na wadanda aka kwaso daga Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa, sun dira a Lagos shekaranjiya Laraba.

Da yake jawabi a wajen taron manema labarai na kwamitin karta kwana na shugaban kasa kan cutar corona, wanda ake gudanarwa kullum, a Abuja, ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeamna, yace za a killace wadanda suka dawo a Otal-Otal a babban birnin tarayya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seventeen + nine =