‘Yan Najeriya 160 Da Suka Makale Sun Taso Daga Amurka Zuwa Abuja

9

Rukunin farko na ‘yan Najeriyan da suka makale a Amurka saboda annobar corona, suna kan hanyarsu ta dawowa gida.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya bayar da rahoton cewa ‘yan Najeriya 160 wadanda suka hada da yara kanana 8, sune a rukunin farko na wadanda za a kwaso.

Zasu dawo a jirgin saman kamfanin jiragen saman Ethiopia, karkashin wani shirin jigila na musamman wanda gwamnatin tarayya ta yi domin ‘yan kasarnan da suka makale a kasashen waje.

Jirgin saman ya taso daga filin jiragen saman Newark da ke birnin New Jersey na Amurkan, kuma ana sa ran isowarsa zuwa filin jiragen saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, yau da rana.

Da saukarsa, za a killace wadanda aka kwaso tsawon kwanaki 14 a Abuja, kafin a barsu su tafi zuwa inda suka nufa cikin kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

six + 13 =