Akalla Mutane 300 Aka Kashe A Wani Rikicin Kabilanci A Sudan Ta Kudu

17

Akalla mutane 300 aka kashe a wani sabon rikicin kabilanci a Sudan ta Kudu, a cewar hukumomi.

Gomman gidaje a jihar Jonglei aka rusa, inda aka wawashe dakin ajiya mallakin kungiyoyin agaji, tare da sace mata da shanu.

Ma’aikatan ceto 3 suna daga cikin wadanda aka kashe.

An sanya hannu akan wata yarjejeniya da nufin kawo karshen yakin basasar kasar na shekaru 6 a watan Fabrairu, amma rikicin kabilanci ya sha barkewa a lokuta da dama tun bayan yarjejeniyar.

An yi amannar cewa mutane 800 ne suka mutu a irin wannan hare-haren tun daga watan na Fabrairu.

Rikicin baya-bayan nan tsakanin makiyaya da manoma, ya fara a ranar Asabar a garin Pieri dake Arewa maso Gabas, lamarin da ya tursasawa dubban mutane arcewa zuwa daji.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 + 5 =