CORONA: Gwamnati Tarayya Tana Tantace Kamfanoni Domin Samar Da Maganin Gargajiya

7

Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya tana tantance kamfanonin cikin gida 19 domin samar da maganin gargajiyan da zai magance cutar corona.

Kamfanonin sun yi ikirari daban-daban, wadanda suka hada da samar da maganin cutar corona kai tsaye zuwa samar da maganin da zai warkar da alamun cutar.

Kamfanonin sun gana da shugabannin ma’aikatar tare da sashen kula da magungunan gargajiya.

Sai dai, an bukaci kamfanonin da su gabatar da samfurin magungunansu zuwa ga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, daga cikinsu za a zabi kamfanoni 3 wadanda za a tallafawa da kudade.

Karamin ministan lafiya, Sanata Mamora, shine ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × five =