Corona: Gwamnatin Kaduna Ta Kara Wa’adin Dokar Kulle Da Sati 2

3
Gwamna Nasir El-Rufai

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kara wa’adin dokar kullen da ta kakaba a jihar domin hana bazuwar cutar coronavirus, da makonni 2.

Amma karin na makonni 2 zai fara daga ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa, a cewar mataimakiyar gwamnan jihar, Dr Hadiza Balarabe, wacce ta sanar da haka a wani jawabi da aka watsawa mazauna jihar.

Ranaku biyun da ake dage dokar a sati, suna nan a ranakun Laraba da Alhamis, a yanzu.

Tace ranaku 3 da za ake dage dokar zasu fara aiki daga ranar 1 ga watan na Yuni, a madadin ranakun Laraba da Alhamis, ranaku 3 na fita zasu fara daga Talata da Laraba da Alhamis.

Tace an dauki wannan matakan da nufin marawa kokarin gwamnati baya, wajen kare lafiyar mazauna jihar, tare da karfafawa jama’a gwiwa wajen jagorancin yaki da cutar corona.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × 1 =