Gwamnatin Tarayya za tayi amfani da otal da otal da makarantu a matsayin guraren killace masu corona

5

Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya zata mayar da otel otel da makarantu zuwa wajen killacewa da kula da marasa Lafiya saboda karancin gadajen asibiti.

Ministan ya bayyana haka ne a jiya alhamis a yayin taron kwamitin karta kwana na shugaban kasa kan cutar corona wanda ya gudana a Abuja.

Ministan ya kara da cewa marasa lafiyar sun kasu zuwa matakai hudu, wanda ya fara daga wadanda suke nuna kananun alamun cutar ko kuma wadanda basa nunawa kwata-kwata zuwa wadanda suke bukatar kulawa ta musamman.

Kazalika ministan yayi bayanin cewa kasar nan ta bayar da rahoton mutuwar mutane 254, wadanda yawancin su mutanene da ke da wasu cututtukan na daban irinsu hawan jini, ciwon suga ko wasu cututtukan da basa yaduwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − four =