Shugaba Buhari ya umarci sojoji su fatattaki ‘yan bindiga bayan an kashe mutane 74 a Sokoto

3

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojoji da su fatattaki ‘yan bindiga a jihar Sokoto.

Umarnin ya biyo bayan hare-haren ranar Laraba da aka kai a yankin karamar hukumar Sabon Birni, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, tare da raunata wasu.

Shugaban kasar ya aika da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Shugaba Buhari ya kara da cewa an kaddamar da wani babban shirin sojoji mai lakabin Operation Accord, domin yakar mahara dake addabar jihoshin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Shugaba Buhari ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa gwamnati ta dage wajen karesu daga hare-haren ‘yan bindiga.

‘Yan bindigar sun kai farmaki kasa da awanni 24 bayan Gwamna Aminu Tambuwal ya ziyarci yankunan kananan hukumomin Sabon Birni da Isa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − thirteen =