An samu sabbin mutane 307 da suka kamu da corona a Najeriya

3

Jumillar yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar corona a Najeriya a jiya Lahadi sun karu zuwa 10,162 bayan hukumar dakile bazuwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da sabbin mutane 307 da suka kamu.

Mutane 14 ne aka bayar da rahoton cutar ta hallaka jiya Lahadi, wanda ya kawo jumillar wadanda aka tabbatar sun mutu sanadiyyar cutar a kasarnan zuwa 287.

An samu raguwar yawan wadanda suka kamu a jiya Lahadi da mutane 307, idan aka kwatanta da mutane 553 da aka bayar da rahoton sun kamu shekaranjiya Asabar.

Hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter jiya da dare cewa an samu sabbin mutane 307 a jihoshi 15. Jihoshin sune Lagos, Babban Birnin Tarayya, Ogun, Kaduna, Oyo, Bayelsa, Gombe, Kano, Delta, Imo, Rivers, Niger, Bauchi, Plateau da kuma jihar Kwara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − four =