Gwamnati Tarayya ta mika yaki da corona ga jihoshi da al’umomi

4

shugaban kwamitin karta kwana na shugaban kasa kan cutar corona, Boss Mustapha, yace gwamnatin tarayya ta mika ragamar yaki da cutar corona zuwa ga jihoshi da al’umomi.

A cewarsa, daga yanzu gwamnatin tarayya za take sa ido ne kawai tare da tsarawa.

Boss Mustapha wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, yayi jawabi a fadar shugaban kasa bayan ‘yan kwamitin karta kwana sun yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayanin halin da ake ciki, tare da tattauna shawarwarinsu akan matakin da za a shiga na sabon shafin yaki da cutar.

A tare da shi lokacin ganawar akwai Ministan Lafiya, Dr. Osagie Ehanire, da jagora na kasa na kwamitin karta kwanan, Dr. Sani Aliyu, da Darakta-Janar na hukumar dakile bazuwar cututtuka ta kasa NCDC, Dr. Chikwe Ihekweazu, da kuma ministan cikin gida, Rauf Aregbesola.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven − 1 =