Jam’iyyar PDP ta lashe zaben Kananan Hukumomi a Benue

7

Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Benue ta lashe zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar ranar Asabar da ta gabata.

Kamar yadda yazo a sakamakon zaben da shugaban hukumar zabe mai zamanta kanta ta jihar, Terso Loko, ya sanar jiya Lahadi, jam’iyyar ta PDP ta yi nasara a dukkanin zabukan kananan hukumomi 23 da mazabu 276 a zaben da aka kammala.

Loko ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa 5 ne suka shiga zaben.

Ya ambaci jam’iyyun da suka hada da APGA da Jam’iyyar Labour da AAC da SDP da kuma PDP.

Babbar jam’iyyar adawa ta APC a ranar Juma’a ta sanar da cewa baza ta shiga zaben ba, wanda ta kira da wasan kwaikwayo.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 − 4 =