‘Yan bindiga sun kashe gomman mutane a wata kasuwar shanu a Burkina Faso

10

An kashe mutane 30 a gabashin Burkina Faso a wani harin ‘yan bindiga kan wata kasuwar shanu.

‘Yan bindiga akan babura sun yi harbi kan mai uwa da wabi a kasuwar dake makare da mutane a garin Kompeinga da rana a ranar Asabar, a cewar shaidun gani da ido da mazauna gari.

Sai dai babu tabbacin wadanda suka kai harin, amma Burkina Faso ta fuskanci karuwar hare-haren ta’addanci da rikice-rikicen kabilanci.

Tashe-tashen hankulan sun tursasawa dubban mutane arcewa daga gidajensu.

Da farko kafafen yada labarai sun bayar da rahoton cewa mutane 20 aka kashe, yayin da suka labarto majiyoyi na cewa yawan mace-macen zai iya karuwa sosai.

A ranar Juma’a akalla mutane 15 aka kashe, lokacin da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka kai farmaki kan ayarin motocin fatake a arewa, kusa da iyakar kasar da Mali.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × two =