Gwamnatin Tarayya ta gargadi gwamnatocin jihoshi dangane da sake bude makarantu

19

Gwamnatin Tarayya ta gargadi gwamnatocin jihoshin dake shirin sake bude makarantu da su watsar da shirin.

Shugaban kwamitin karta kwana na shugaban kasa kan cutar corona kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayar da gargadin yayin taron manema labarai na kwamitin karta kwana na shugaban kasa wanda aka gudanar a Abuja.

Boss Mustapha yace akwai hadari a sake bude makarantu, gidajen kallo, filayen wasanni da sauran guraren da mutane ke taruwa sosai.

A makon da ya gabata, gwamnatin jihar Kano ta sake bude gidajen kallo. Akwai rahotannin da aka samu jiya Litinin cewa gwamnatin jihar Cross River wacce har yanzu ba a samu mai cutar corona ba, tana shirin sake bude makarantu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 1 =