Gwamnatin Tarayya tace har yanzu dokar hana bulaguro tsakanin jihoshi na aiki

6

Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘yan Najeriya cewa har yanzu dokar hana haramta bulaguro daga wata jiha zuwa wata tana aiki.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya hori jami’an tsaro da su tabbatar da cewa jama’a na kiyayewa da dokar.

Boss Mustapha wanda shine shugaban kwamitin karta kwana na shugaban kasa kan cutar corona yayi jawabi yayin taron manema labarai na kwamitin wanda aka gudanar a Abuja jiya Litinin.

Gwamnatin tarayya ta hana tafiye-tafiye tsakanin jihoshi, a kokarin dakile bazuwar cutar corona a fadin kasarnan.

Ana sa ran janye dokar a ranar 21 ga watan Yunin da muke ciki, kamar yadda mai taimakawa shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai, Bashi Ahmad, ya sanar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × three =